logo

HAUSA

Ma’aikatar harkokin wajen Sin: Komai tsaikon da aka kawowa kasar Sin ba zai hana ci gaban harkokin kimiyya da fasaharta ba

2022-08-10 20:54:15 CMG Hausa

Kwanan nan ne shugaban kasar Amurka Joe Biden, ya sanya hannu kan doka mai alaka da sassan na’urorin laturoni na Chips, da sauran ayyukan kimiyya ta shekara ta 2022.

Game da wannan batu, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a yau Laraba cewa, kasarsa tana tsayawa tsayin daka, wajen maida hankali a fannin samar da ci gaban kasa da na al’umma, kana, komai tsaiko ko matsin lambar da aka sanyawa kasar, ba za su hana ci gaban kimiyya da fasaha gami da sana’o’in kasar ba.

Wang ya ce, dokar ta ce wai tana so ta kara karfin yin takara na kimiyya da fasahar Amurka, da sana’ar kera sassan na’urorin laturoni ta kasar, amma za ta samar da dimbin tallafin kudi ga wannan sana’ar dake cikin gida, da aiwatar da wasu manufofi mabambanta don tallafawa sana’ar, ciki har da kawo cikas ga wasu kamfanoni, don su zuba jari ko gudanar da kasuwanci a kasar Sin, da gudanar da hadin-gwiwa tsakanin su da kamfanonin kasar Sin a fannin kimiyya da fasaha, al’amarin da zai lalata aikin samar da rukunin sassan na’urorin laturoni na duniya, da cinikayyar kasa da kasa. Don haka, kasar Sin ta nuna rashin yardar ta kan wannan doka. (Murtala Zhang)