logo

HAUSA

Ana tuhumar wani baAmurke da kisan wasu musulmai a jihar New mexico

2022-08-10 09:20:22 CMG Hausa

Ana tsare tare da tuhumar wani baAmurke mai shekaru 51 da ake zargi da kisan wasu maza musulmai, akalla 2 daga cikin 4 da aka kashe yayin wani harbin kwantan bauna, cikin watanni 9 da suka gabata a Albuquerque, birni mafi girma a jihar New Mexico dake kudancin Amurka.

Shugaban ‘yan sandan jihar Harold Medina, ya wallafa jiya a shafin twitter cewa, ‘yan sanda sun bibiyi motar da suka yi ammana an yi amfani da ita wajen kisan wani musulmi a baya-bayan nan a birnin, kuma an kama tare da tsare direban da shi ne mutum na farko da ake zargi da aikata kashe-kashen.

Maza musulmai 4 ne aka kashe yayin wani harbin kwantan bauna a birnin, tun cikin watan Nuwamban bara, kuma an harbe 3 daga cikinsu har lahira ne cikin kwanaki 10, lamarin da ya ja hankalin al’ummar kasar da ma na duniya baki daya.

Kafafen watsa labarai na kasar na ganin cewa, birnin na gab da zama wuri mafi yawan kisan mutane a bana. (Fa’iza Mustapha)