logo

HAUSA

Kasar Sin ta yi kira da a taimakawa kasashe masu tasowa don inganta karfinsu na yaki da ta'addanci

2022-08-10 11:09:07 CMG Hausa

              

Jiya ne, zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Zhang Jun ya yi jawabi a yayin taron bainar jama'a da kwamitin sulhu na MDD ya kira kan "Barazanar ayyukan ta'addanci ga zaman lafiya da tsaron kasa da kasa”, inda ya bayyana matsayin kasar Sin, game da yaki da ta'addanci, kana ya yi kira da a mai da hankali kan taimakawa kasashe masu tasowa, musamman kasashen Afirka, wajen inganta karfinsu na yaki da ayyukan ta'addanci.

Zhang Jun ya ce, rahoton da babban sakataren MDD ya fitar na nuna cewa, yankuna biyu cikin uku da masu da’awar kafa "Daular Musulunci" suka fi gudanar da ayyukansu, suna Afirka ne. Don haka, ya kamata, kasashen da ke wajen yankin, su karfafa hulda da hadin gwiwa da kasashen Afirka, tare da tattauna yadda za a warware kalubalen da ake fuskanta a fannin dabaru, da kudi da karfin ayyukan yaki da ta'addanci da kasashen Afirka suke fuskanta karkashin tsarin MDD.

Zhang Jun ya kara da cewa, kasar Sin ta taimaka wa kasashe masu tasowa, ta hanyar shiga a dama da ita a hadin gwiwar kasa da kasa kan yaki da ta'addanci, musamman kasashen Afirka, wajen inganta karfinsu na rigakafi da yaki da ayyukan ta'addanci.

Bugu da kari, kasar Sin za ta ci gaba da ba da taimako da goyon baya ga kasashen da ke kan gaba wajen yaki da ayyukan ta'addanci irinsu Afirka da yankin tsakiyar Asiya, domin kara karfinsu na yaki da ta'addanci, ta hanyar daukar matakai na zahiri, da ba da gudummawa wajen tinkarar barazanar ayyukan ta'addanci yadda ya kamata, da kiyaye zaman lafiya da tsaro a yankin. (Ibrahim Yaya)