logo

HAUSA

Wang Wenbin: Sin za ta mayar da martani idan har Amurka ta ci gaba da takalarta

2022-08-10 21:04:16 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ja kunnen kasar Amurka, da ta yi watsi da aniyar amfani da batun Taiwan wajen gallazawa kasar Sin, yana mai cewa, idan har Amurka ta sake takalar Sin, kasar Sin din za ta maida kakkausan martani.

Wang, wanda ya bayyana hakan yayin taron manema labarai na Larabar nan, ya ce ya zama wajibi Amurka, ta kaucewa rura wutar rikici tun kafin lokaci ya kure. Ya kuma sake jaddada yadda ziyarar baya bayan nan ta kakakin majalissar wakilan Amurka Nancy Pelosi a yankin Taiwan, ta keta ka’idar nan ta kasar Sin daya tak a duniya, kuma wata tsokana mai matukar hadari.

Bugu da kari, Wang ya kare matakan da Sin ke aiwatarwa, biyowa bayan ziyarar Pelosi a yankin Taiwan, a matsayin wadanda suka dace, kana sun biyo bayan matakan tsokana da Amurka ta aikata. (Saminu Alhassan)