logo

HAUSA

Sin: Ya kamata Amurka ta yi amfani da zarafi mai kyau don cimma matsaya daya kan batun nukiliyar Iran

2022-08-09 11:23:17 CMG HAUSA

 

Kasashen Amurka da Iran sun koma teburin tattaunawa kan aiwatar da cikakkiyar yarjejeniyar da aka cimma kan batun nukiliyar kasar Iran bayan watanni 5 da aka maido da shawarwarin. Wakilin Sin game da batun, kana zaunananen wakilin Sin a ofishin MDD dake Vienna, Wang Qun ya bayyana a jiya Litinin cewa, a halin yanzu, ana fuskantar wata dama mai kyau kan wannan tattaunawa, yana kuma fatan Amurka da ta yanke shawara a siyasance, don ingiza cimma matsaya daya a shawarwarin.

Wang Qun ya nuna cewa, ci gaba da yin shawarwarin na nuna cewa, nacewa wajen daidaita bambance-bambance ta hanyar tattaunawa da yin shawarwari, ita ce hanya daya tilo da ta dace. Yana kuma fatan dukkan bangarori za su yi amfani da damar da ake da ita a halin yanzu, da mutunta ra’ayoyi da muradun juna, ta samar da hanyoyin warware matsalolin da ba a kai ga daidaitawa ba a shawarwarin, ta yadda za a kai ga cimma nasarar shawarwarin.

A cewar Wang Qun, kamata ya yi Amurka, a matsayinta na wadda ta fara haddasa rikicin nukiliyar Iran, ta fahimci halin da ake ciki a zahiri, ta nuna gaskiya, tare da yin watsi da ra’ayi na siyasa da "ma'auni biyu" kan batun hana yaduwar makaman nukiliya, ta yadda za a ingiza cimma matsaya a shawarwarin tabbatar da yarjejeniyar da aka cimma tsakanin bangarorin biyu. (Amina Xu)