logo

HAUSA

Wani gidan adana kayan tarihi na London ya amince da mayar da kayan tarihi 72 ga kasar Nijeriya

2022-08-08 11:13:03 CMG Hausa

Gidan adana kayan tarihi na Horniman na birnin London dake kasar Birtaniya ya bayyana a gun taron manema labaru a jiya cewa, zai mayar da kayan tarihin masarautar Benin 72 ga kasar Nijeriya, ciki har da na tagulla, da kayan haurin giwa, mafifici, da kwando da sauransu.

A shekarar 1897 ne, sojojin mulkin mallaka na kasar Birtaniya suka kai hari masarautar Benin, inda suka kone tsohon birnin kasar Benin tare da kwashe kayan al’adun gargajiya na wurin, lamarin da ya yi sanadiyar asarar dubban kayayyakin tarihi.

Shugabar amintattu na gidan adana kayan tarihi na Horniman, Eve Salomon ta bayyana cewa, shaidun sun tabbatar da cewa, an kwace wadannan kayan tarihi ta karfin tuwo, hukumomin nazari kan kayayakin tarihi, sun goyi bayan ra’ayin gidan adana kayan tarihi na Horniman cewa, ya kamata a mayarwa Najeriya wadannan kayayyaki, kuma hakan abu ne da ya dace. (Zainab Zhang)