logo

HAUSA

Ma’aikatar harkokin wajen Sin: Sanarwar kasashen Amurka da Australiya da Japan ta sabawa doka

2022-08-08 20:27:03 CMG Hausa

Kwanan nan ne, kasashen Amurka da Australiya da Japan, sun fitar da wata sanarwar hadin-gwiwa, inda suka gindaya sharadi game da aiwatar da “manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya”.

Game da hakan, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a yau Litinin cewa, wasu kasashe kalilan sun kara gindaya wasu sharudda, game da aiwatar da manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, da zummar jirkita gaskiya, da bata wannan manufa, al’amarin da ya sabawa doka, wanda kasar Sin ta ki yarda da shi.

Rahotanni sun ce, kasashen Amurka, da Australiya, da Japan, sun fitar da wata sanarwar hadin-gwiwa bayan da suka yi shawarwari, inda suka sake jaddada cewa, manufofinsu game da kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, da matsayinsu kan batun Taiwan ba su canza ba, kana, sun kara wata jimla bayan “kasancewar kasar Sin daya tak a duniya” dake cewa, “a yanayin da ya dace”.

Bugu da kari, game da kalaman kakakin fadar White House dake Amurka, da suka shafi batun yankin Taiwan, Wang Wenbin ya ce, dalilan da bangaren Amurka ya fitar, ba za su iya boye ainihin halin da ake ciki ba, wato Amurka ce take yunkurin sauya halin da ake ciki a mashigin tekun Taiwan, da ta’azzara halin da ake ciki, kuma Amurka ce take yunkurin hura wutar rikici, kana Amurka ta gaza wajen sauke nauyin dake wuyanta. (Murtala Zhang)