logo

HAUSA

Jam’iyyun kasa da kasa sun yi tir da Amurka kan neman tada zaune tsaye a yankin Taiwan

2022-08-08 11:11:30 CMG Hausa

Shugabar majalisar wakilai ta kasar Amurka Nancy Pelosi, ta ziyarci yankin Taiwan, duk da babbar adawar da kasar Sin ta nuna kan wannan batu. Jam’iyyun siyasa na kasashe da dama na duniya, sun yi tir da matakin Amurka na neman tayar da tada zaune tsaye da take yi a yankin Taiwan da cewa ko kadan bai dace ba.

Jam’iyyar Islamic Coalition ta kasar Iran wato ICP ta fitar da sanarwa, inda a cikinta, ta yi Allah wadai da matakin da jami’an gwamnatin Amurka suka dauka na neman tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin, da kawo illa ga cikakken yankin kasar Sin. Wannan a cewarta, shaida ce, na yadda kasar Amurka ke tsoma baki a wurare daban daban na duniya, kuma hakan babu abin da zai haifar, sai dai tsananta rikici da tada zaune tsaye.

Kasar Amurka tana da yunkurin yin amfani da batun yankin Taiwan da gangan, don illata moriyar kasar Sin. Don haka, wasa da wuta da Amurkar ke yi, zai tsananta rikici ne kawai a cikin gidan Amurka.

Ita ma jam’iyyar Socialist ta jama’ar kasar Mexico, ta bayar da sanarwa cewa, halin rashin da'a da girman kai na Amurka, ya sake saba manufar Sin daya tak a duniya da ma kudurorin MDD da suka dace. (Zainab)