logo

HAUSA

Ziyarar Nancy Pelosi a yankin Taiwan ta tsananta halin da yankin ke ciki tare da zubar da kimar Amurka a duniya

2022-08-08 08:01:21 CMG HAUSA

DAGA MINA

Kwanan baya, kakakin majalisar wakilan kasar Amurka Nancy Pelosi ta kai ziyara yankin Taiwan na kasar Sin, matakin da ya sabawa ka’idar “kasar Sin daya tak a duniya” da sanarwoyin hadin gwiwa guda uku da Sin da Amurka suka cimma. Yau “Duniya a zanen MINA”, na bayani ne kan burin da Pelosi ke neman cimmawa a wannan ziyararta.

Nancy Pelosi ta yi ikirarin cewa, ba za ta manta da alkawarin da ta yi game da yankin ba, matakin da ya baiwa ‘yan aware na Taiwan damar neman taimako daga kasashen yamma, a yunkurin neman ballewar yankin daga kasar Sin. Amma ainihin burinta shi ne fakewa da batun yankin Taiwan, don neman samun kuri’u a zaben tsakiyar wa’adi za a yi a kasar Amurka, tare da kawar da hankalin al’umma daga abubuwan kunya da iyalanta suka aikata, ta yadda za ta kiyaye kujerarta a majalisar, tare da  samun karin moriya.

Ziyarar Pelosi a yankin Taiwan mai cike da burin siyasa, ba za ta kawowa yankin demokuradiyya ba, a maimakon haka, sai ma ya tsananta halin da ake ciki a yankin. ‘Yan siyasar Amurka irinta Pelosi wadanda suka ci amanarsu don neman cimma burinsu na siyasa, sun zubar da kimarsu a duniya. Kuma daga kashe, za su girbi abin da suka shuka. (Amina Xu)