logo

HAUSA

Gwamnatin riko da ‘yan adawa na kasar Chadi sun cimma yarjejeniyar zaman lafiya a Doha

2022-08-08 16:08:45 CMG Hausa

Wakilan gwamnatin riko na Chadi da na kungiyoyin adawa 42, sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a birnin Doha na Qatar, a yau Litinin.

Rattaba hannu kan wannan yarjejeniya ya shimfida tubalin ga shirin tattauna batutuwan kasar da aka shirya gudanarwa ranar 20 ga wata a N’Djamena, babban birnin kasar. Bisa tanadin yarjejeniyar, bangarorin za su tsagaita bude wuta zuwa lokacin gudanar taron. (Fa’iza Msutapha)