logo

HAUSA

Jami’an tsaro a Nijeriya sun halaka ‘yan bindiga tare da ceto mutanen da suka sace

2022-08-08 11:11:40 CMG Hausa

 

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina dake arewacin Nijeriya, ta ce jami’anta da na soji, sun halaka ‘yan bindiga 8, tare da ceto mutane 6 da suka sace.

Kakakin rundanar Gambo Isa, ya bayyana cikin wata sanarwa a jiya cewa, ‘yan sanda sun gudanar da ayyukan ne da safiyar ranar Asabar bisa dogaro da bayyanan sirri, inda kuma suka dakile yunkurin ‘yan bindiga tare da ceto mutane 6 da suka sace.

Ya kara da cewa, a washegari ranar Lahadi, wani harin soji ta sama a wannan wuri kuma, ya yi sanadin halaka ‘yan bindiga 8. (Fa’iza Mustapha)