logo

HAUSA

Mahukuntan Sudan sun gabatarwa jakadan Chadi korafi bisa kisan fararen hula a jihar Dafur ta yamma

2022-08-07 16:59:14 CMG Hausa

Mahukuntan kasar Sudan, sun gabatarwa jakadan kasar Chadi korafi, bisa kisan fararen hula a kalla 18, da ake zargin wasu dakarun kasar Chadi da aikatawa a jihar Dafur ta yamma.

Kamfanin dillancin labarai na SUNA, ya rawaito cewa, yayin ganawa da jakadan na kasar Chadi a Sudan, ministan harkokin wajen Sudan Ali Al-Sadiq, ya bukaci gwamnatin Chadi da ta gaggauta kamo dakarun da suka hallaka fafaren hular su 18, tare da yin awon gaba da rakuma 220, daga wani kauye dake kan iyakar kasashen biyu.

Da yake maida jawabi game da lamarin, jakadan na Chadi ya ce kasar ba za ta yi kasa a gwiwa ba, wajen tabbatar da ta aiwatar da dukkanin matakai na bunkasa alakar ta da Sudan, a fannonin tsaro da wanzar da zaman lafiya da daidaito, kuma ba za ta bar wata kafa ta gurgunta alakar dake tsakanin sassan 2 ba.

Cikin wata nasarwa da majalissar koli ta rikon kwaryar kasar Sudan ta fitar a ranar Juma’a, ta ce wasu dakaru dauke da makamai, sun kutsa kai iyakar kasar daga Chadi, inda suka hallaka a kalla fararen hula 18, tare da sace rakuma 220.  (Saminu Alhassan)