logo

HAUSA

Wakilin Sin ya ki amincewa da zargin da Amurka ta yi kan manufofin makamashin nukiliyar kasar Sin

2022-08-07 17:59:30 CMG Hausa

A halin yanzu, ana gudanar da babban taro karo na 10, na dudduba yarjejeniyar haramta yawaitar makaman nukiliya, a hedikwatar Majalisar Dinkin Duniya dake birnin New York, inda a kwanan nan, wakilin kasar Amurka ya yi zargin cewa, wai kasar Sin tana gaggauta habaka makaman nukiliyarta, da kin gudanar da shawarwari tare da bangaren Amurka, kan batun takaita amfani da makaman nukiliya.

Game da irin wannan zargi da Amurka ta yi ba gaira ba dalili, wakilin kasar Sin Ding Tongbing, ya bayyana kin amincewa. Ding ya bayyana cewa, kasar Sin bata yarda da zargin Amurka, kan manufofin Sin game da makamashin nukiliya. A cewarsa, zargin na Amurka ba zai canja hakikanin gaskiya ba, wato a matsayinta na babbar kasa mai yawan mallakar makaman nukiliya, har yanzu, ma’ajiyar makaman nukiliyar ta na kara kawo barazana ga zaman lafiyar dukkanin duniya. Bugu da kari, Amurka ta kara daukar wasu matakai, wadanda suka haifar da babbar illa ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a shiyya-shiyya da ma duniya baki daya.

Ding ya kara da cewa, kasar Sin ta dade da kokarin takaita mallakar makaman nukiliya, don biyan bukatun tabbatar da zaman lafiya da tsaron kan ta kadai.

Jami’in ya kara da cewa, kasar Sin ba ta taba shiga takarar makaman nukiliya a lokacin baya ba, kuma ba za ta yi hakan a nan gaba ba. Ya ce makasudin kasar Sin na mallakar makaman nukiliya shi ne, hana sauran kasashe su yi amfani da na su kan kasar Sin. Kuma muddin ba su yi amfani da makaman nukiliya kan kasar Sin ba, babu bukatar daukar nata makaman nukiliyar a matsayin barazana, kuma, ba za su ji irin wannan barazana daga kasar Sin ba. (Murtala Zhang)