logo

HAUSA

Wang Yi ya yi tsokaci kan matsayar Sin a batun tekun kudancin kasar

2022-08-06 16:00:12 CMG Hausa

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya halarci taron ministocin harkokin wajen kasashen dake yankin gabashin Asiya karo na 12 a birnin Phnom Penh, fadar mulkin kasar Kambodia, jiya Juma’a 5 ga wata, inda ya yi tsokaci kan matsayar da kasar Sin ta dauka kan batun da ya shafi tekun kudancin kasar, tare da yin tir da kulawar da Amurka ta nuna.

Wang Yi ya bayyana cewa, matsayar kasar Sin kan tekun kudanci tana bisa doron doka da tarihi, kuma kasar Sin ba ta taba sauya matsayarta ba, wato kasar Sin da kasashe mambobin kungiyar ASEAN, sun daidaita sabanin dake tsakaninsu ta hanyar tattaunawa bisa “sanarwar bangarorin da tekun kudancin ya shafa”. Ya ce a cikin ‘yan shekarun da suka gabata, kasar Sin da kasashen ASEAN sun yi kokari tare, domin tabbatar da kwanciyar hankali a tekun, ta yadda za su samu ci gaba tare.

Wang Yi ya kara da cewa, a halin da ake ciki yanzu, wadda ke kawo hadari ga kwanciyar hankalin yankin tekun kudanci ita ce Amurka, duk da cewa, ba ta taba nuna rashin amincewa kan matsayar kasar Sin a yankin tekun ba cikin lokaci mai tsawo, amma yanzu ta musunta matsayar kasar Sin ta kowacce fuska, kuma matakin da ta dauka ba shi da dalili ko tushen doka ko kadan, yana mai cewa, idan wata babbar kasa ta sauya manufarta kamar yadda take so bisa bukatun siyasa, shin ina amana da kimarta suke?  (Jamila)