logo

HAUSA

Wang Yi ya yi cikakken bayani kan matsayar Sin game da yankin Taiwan

2022-08-06 15:50:32 CMG Hausa

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya kira taron ganawa da manema labarai a yammacin jiya, bayan ya halarci tarukan ministocin harkokin wajen kasashen gabashin Asiya da aka shirya a birnin Phnom Penh, fadar mulkin kasar Cambodia domin kyautata hadin gwiwa a tsakaninsu.

Yayin taron manema labaran, Wang Yi ya ce, “Shugabar majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosy, ta yi watsi da adawar gwamnatin kasar Sin, ta kai ziyara yankin Taiwan, bisa amincewar gwamnatin kasar Amurka”.

Ya ce a bayyane yake cewa, ziyararta ta keta ‘yancin mulkin kan kasar Sin, kuma ta tsoma baki cikin harkokin gidan kasar, haka kuma ta sabawa alkawarin gwamnatin Amurka, tare kuma da lahanta zaman lafiya da kwanciyar hankali a zirin Taiwan. Don haka, tabbas kasar Sin ta mayar da martani ta hanyar daukan matakai masu karfi da suka dace bisa matsayar adalci. Kuma ko shakka babu, atisayen soja da rundunar sojojin kasar Sin take yi a fili, ya dace da dokar kasar, da ta kasa da kasa, da kuma ka’idojin kasa da kasa.

A cewar Wang Yi, manufar ita ce, yi wa masu tayar da tarzoma kashedi, da kuma hukunta masu neman ‘yancin kan Taiwan. Haka kuma, za a ci gaba da daukar matakan da suka dace domin kiyaye ‘yancin mulkin kan kasar Sin da yankunan kasar, da murkushe yunkurin Amurka na hana ci gaban kasar Sin bisa fakewa da batun yankin Taiwan, tare kuma da murkushe makarkashiyar mahukuntan yankin Taiwan na neman ‘yancin kai bisa dogaro da goyon bayan Amurka.

Bugu da kari, Wang Yi ya ce kasar Sin na kokarin kare dokar kasa da kasa, da ka’idar huldar dake tsakanin kasa da kasa, musamman ma ka’idar rashin tsoma baki cikin harkokin gidan sauran kasashe ta MDD, yana mai cewa, “Idan aka yi watsi da ka’idar, manyan kasashe kamar Amurka za su zalunci kananan kasashe kamar yadda suke so, amma ba zai yiyu kasar Sin ta amince da faruwar irin wannan al’amari ba, kuma ya dace kasashen duniya su hada kai domin hana koma bayan wayewar kan bil Adam.” (Jamila)