logo

HAUSA

Kasar Sin na gudanar da atisayen soji a Rawayen teku da tekun Bohai

2022-08-06 18:53:34 CMG Hausa

Hukumar kula da sufurin jiragen ruwa ta kasar Sin, ta ce kasar zata gudanar da atisayen harba makamai daga yau 6 ga wata zuwa 15 ga wata, a yankin kudancin Rawayen teku dake gabashin kasar.

Sanarwar da hukumar ta fitar, ta ce kazalika a yau Asabar, ana gudanar da atisayen soji a bangaren arewacin tekun Bohai, duk a gabashin kasar Sin. (Fa’iza Mustapha)