logo

HAUSA

Amurka ta ayyana cutar kyandar biri a matsayin larurar dake bukatar kulawar gaggawa

2022-08-05 10:31:59 CMG Hausa

 

Gwamnatin kasar Amurka, ta ayyana cutar kyandar biri a matsayin larurar dake bukatar kulawar gaggawa, hakan na zuwa ne mako guda, bayan da hukumar lafiya ta duniya WHO ta ayyana kyandar birin a matsayin cutar dake bukatar daukin gaggawa a duniya.

Da yake karin haske ga manema labarai kan batun, sakataren sashen ba da hidimar lafiyar al’umma na kasar Amurka Xavier Becerra, ya ce gwamnatin ta shirya daukar matakai na gaba, a fannin shawo kan cutar ta kyandar biri, tana kuma fatan daukacin Amurkawa za su dauki wannan cuta da muhimmanci.

A ranar Alhamis, mahukuntan Amurka suka tabbatar da harbuwar sama da mutum 6,600 da cutar kyandar biri, adadin da ya kai kusan kaso 25 bisa dari na jimillar mutane 25,800 da suka harbu da annobar a duniya baki daya.  (Saminu Alhassan)