logo

HAUSA

Ma’aikatar harkokin wajen Sin ta aike da sammaci ga wasu jakadun kasashen Turai da kungiyar EU don nuna rashin jin dadinta

2022-08-05 14:46:41 CMG Hausa

Jiya ne, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Deng Li ya aike da sammaci ga wasu jakadun kasashen Turai da kungiyar EU da ke kasar Sin, don nuna rashin jin dadinta kan yadda ministan harkokin wajen kasashe mambobin kungiyar G7 da babban wakilin kungiyar EU mai kula da harkokin diplomasiyya da tsaro suka bayar da sanarwar nuna halin ko-in-kula kan batun yankin Taiwan na kasar Sin.

Deng ya bayyana cewa, sanarar da ministocin kasashen kungiyar G7 da kuma babban wakilin suka bayar, sun jirkita hakikanin shaidu, wadanda suka mayar da fari baki. Wannan tamkar tsoma baki ne a harkokin cikin gidan kasar Sin, da tsokanar siyasa. Wannan lamari tamkar aike mummunan sako ne ga ’yan a-waren yankin Taiwan. Don haka, kasar Sin ta nuna adawa da rashin jin dadinta matuka.

Deng ya kara da cewa, manufar kasar Sin daya tak a duniya, wata babbar ka’ida ce da kulla dangantaka a tsakanin kasa da kasa, wadda ta samu amincewar gammayar kasashen duniya. Haka kuma wannan manufa, ita ce tushen cudanyar Sin da sauran kasashe a siyasance, kuma babu wanda zai kalubalance ta. (Kande Gao)