logo

HAUSA

Antonio Guterres ya nuna damuwa game da bukatar ficewar dakarun MONUSCO daga jamhuriyar dimokaradiyyar Congo

2022-08-05 10:50:11 CMG Hausa

 

Babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya bayyana rashin jin dadin sa, bisa umarnin da mahukuntan jamhuriyar dimokaradiyyar Congo suka bayar, na ficewar dakarun wanzar da zaman lafiya na rundunar MONUSCO daga kasar.

Babban magatakardar MDDr ta bakin kakakin sa Stephane Dujarric, ya ce wakilin MDD a kasar yana hutun aiki, lokacin da wasu sojojin rundunar ta MONUSCO suka bude wuta kan fararen hula, kuma al’amura sun ta’azzara a halin da ake ciki yanzu.

Dujarric ya shaidawa manema labarai hakan a jiya Alhamis, yana mai cewa, tuni aka fara gudanar da bincike game da harbin da dakarun suka yi a ranar Lahadin karshen mako, kuma nan da ‘yan kwanaki, za a kai ga fitar da bayanan farko game lamarin. (Saminu Alhassan)