logo

HAUSA

Ma’aikatar harkokin wajen Sin ta sanar da matakan martani ga ziyarar da Pelosi ta kai Taiwan

2022-08-05 19:36:27 CMG Hausa

A yau Alhamis, ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, ta sanar da cewa za a soke shirin da aka yi na wayar tarho tsakanin kwamandojin rundunonin sojin kasashen Amurka da Sin da kuma ganawar da za a yi tsakanin ma’aikatunsu na tsaro, tare da sauran wasu matakai.

Haka zalika, kasar Sin ta yanke shawarar kakabawa Pelosi tare da iyalanta takunkuman da suka dace da tanadin dokokin jamhuriyar jama’ar kasar Sin.

Wannan matakin martani ne da Sin ta dauka, saboda nacewar da kakakin majalisar wakilan Amurka ta yi, wajen ziyartar yankin Taiwan, duk da adawa da korafin da kasar Sin ta gabatar. (Fa’iza Mustapha)