logo

HAUSA

Kasar Sin ta harba tauraron dan Adam na farko na sanya ido kan sinadarin Carbon

2022-08-04 16:08:25 CMG Hausa

 

Da karfe 11 da mintoci 8 na safiyar yau ne, kasar Sin ta yi nasarar harba tauraron dan Adam na sanya ido na farko kan sinadarin Carbon, a kokarin kiyaye muhallin halittu da suka shafi kasa, ta hanyar amfani da rokar dakon kaya samfurin “Long March-4B” . 

Tauraron dan Adam din mai suna Jumang, zai ba da hidimomi a fannonin sanya ido kan yawan albarkatun kwal, da binciken albarkatun halittu, da tantance manyan ayyukan kasar Sin da suka shafi muhallin hallittu, ta yadda kasar Sin za ta kara karfinta na fada-a-ji a fannin tinkarar matsalar sauyin yanayin duniya.(Kande Gao)