logo

HAUSA

Wang Yi Ya Yi Tir Da Sanarwar G7 Game Da Batun Yankin Taiwan Na Kasar Sin

2022-08-04 20:32:36 CMG HAUSA

DAGA CMG HAUSA

Yau Alhamis, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang yi ya halarci taron ministocin harkokin wajen kasashen nahiyar gabashin Asiya da aka gudanar a Phnom Penh, hedkwatar kasar Gambodia, inda ya yi tir da sanarwar G7 game da batun yankin Taiwan na kasar Sin.

A cewar Wang Yi, sanarwar da G7 ta fitar ta mai da fari baki da jirkita gaskiya, kuma ta tsoma baki cikin matakai masu dacewa da Sin take dauka wajen kiyaye tsarin mulkinta da cikakken yankinta, Abin da ya fusata jama’ar Sinawa matuka. (Amina Xu)