logo

HAUSA

Ana zaton wuta a makera..

2022-08-03 17:27:05 CMG HAUSA

 

Daga Ibrahim Yaya

A kwanakin baya ne, aka bude taron kasa da kasa kan cutar kanjamau wato AIDS a birnin Montreal na Canada, taron dake zama irinsa mafi girma kan cutar a duniya, baya kasancewarsa wani muhimmin dandali na yayata matakan kariya da magance cutar.

Galibi masana kimiyya da masu fafutuka daga sassa daban-daban na duniya, su kan yi amfani da wannan dama, wajen tattauna batutuwan da suka shafi yaki da cutar ta kanjamau.

Sai dai duk da muhimmancin wannan taro, a bana, daruruwan mahalarta daga nahiyar Afrika, ba su samu damar halarta ba kamar yadda aka tsara, saboda wasu manufofi na nuna wariya wajen bada takardun iznin shiga kasar ta Canada wato visa da gwamnatin kasar Canada ta bullo da su.

Wasu masu ruwa da tsaki kan yaki da cutar kanjamau da suka halarci taro, sun bayyana bacin ransu kan wannan mataki da mai masaukin taron, wato kasar Canada ta dauka. Wai ana zaton wuta a makera, sai ta tashi a masaka.

A baya ana zargin kasashen yamma da nuna wariya da kyama da neman bata sunan kasashe da ma dakushe ci gabansu, sai ga shi irin wannan mummunan dabi’ar ta bulla a kasa kamar Canada.

Wannan ne ma ya sa, masu fafutuka ke cewa, bai kamata a rika gudanar da irin wannan taro mai muhimmanci dake da nufin kare rayuwar al’umma a kasar dake nuna wariyar launin fata ba.

Masu zanga-zanga ma sun bayyana adawa da matakin gwamnatin Canada, na hana daruruwan mahalarta taron shiga kasar, galibinsu daga Afrika, saboda rashin daidaiton da ya kai ga karuwar yaduwar cutar. Suna masu bayyana cewa, ya kamata tarukan duniya kan yaki da cutar kanjamau, su tabbatar da ana damawa da kwararru daga yankunan da suka fi fama da cutar.

Wani abin takaici shi ne, gwamnatin Canada dai ba ta bayyana dalilanta na hana visar shiga kasar ba, amma wasu daga cikin wadanda ta hanawa visar, sun ce wai kasar ba ta yarda cewa, za su koma kasashensu bayan an kammala taron ba. Zato dai zunubi, ko da ya kasance gaskiya.

Masu fashin baki dai na fatan za a daina amfani da wasu matakai marasa dacewa, wajen mayar da hannun agogo baya, a kokarin da ake yi na kiyaye lafiyar al’ummar duniya. (Ibrahim Yaya)