logo

HAUSA

Jam’iyyun siyasa a kasashe da dama sun bayyana adawarsu da ziyarar Pelosy a Taiwan

2022-08-03 19:24:47 CMG Hausa

Sama da jam’iyyun siyasa 60 a kasashe sama da 40, cikinsu har da Masar da Bangladesh da Afrika ta kudu, sun bayyana adawa mai karfi da ziyarar da kakakin majalisar wakilan Amurka, Nancy Pelosy ta kai yankin Taiwan.

Jam’iyyun sun bayyana adawar ne ta hannu ofishin kula da harkokin waje na kwamitin kolin JKS, inda suka ce sun yi ammana cewa, wannan yunkuri, ya yi matukar keta ‘yancin kan kasar Sin da mallakar yankunanta, haka kuma barazana ce ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin zirin Taiwan. Dukkan jam’iyyun sun kuma jaddada nacewa ga manufar Sin daya tak a duniya, tare da kira ga Amurka ta daina katsalandan cikin harkokin gidan Sin. (Fa’iza Mustapha)