logo

HAUSA

Wang Yi: Duk wanda ke neman keta manufar “kasar Sin daya tak a duniya” zai dandana kudar sa

2022-08-03 15:17:01 CMG Hausa

Yau Laraba, yayin da yake halartar taron ministocin harkokin wajen kungiyar tarayyar kasashen kudu maso gabashin Asiya ko (ASEAN) a kasar Kambodia, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya bayyana cewa, ziyarar da kakakin majalissar wakilan Amurka Nancy Pelosi ta kai yankin Taiwan ta kasance rashin hankali. Kana, duk wanda ke neman keta manufar “kasar Sin daya tak a duniya” zai dandana kudarsa.

A safiyar yau Laraba ne aka bude taron ministocin harkokin wajen kungiyar tarayyar kasashen kudu maso gabashin Asiya ta ASEAN karo na 55, a birnin Phnom Penh, fadar mulkin kasar Kambodia. (Maryam)