logo

HAUSA

Za a kaddamar da sashen hidimomin wasanni na bikin cinikayyar hidimomi

2022-08-03 13:47:59 CMG Hausa

Kasancewarsa daya daga cikin sassan musamman guda tara da aka kebe, wajen bikin cinikayyar hidimomi na kasa da kasa na shekarar 2022, za a kaddamar da sashen baje kolin hidimomin wasanni a farkon watan Satumba mai zuwa, a lambun masana’antu na Shougang da ke birnin Beijing.

A gun taron manema labarai da aka kira a jiya Talata, an ce, sashen baje kolin hidimomin wasanni shi ne mafi fadi a harabar filin baje kolin harkoki a bikin na wannan karo. Kawo yanzu kuma, akwai shirye-shirye da dama da suka cimma yarjejeniya a sashen hidimomin wasanni, wadanda kudinsu ya kai kudin Sin yuan biliyan 5.35.

Chen Jie, kakakin hukumar kula da harkokin wasanni na birnin Beijing ya bayyana cewa,“An karkasa sashen baje kolin hidimomin wasanni zuwa gida takwas, ciki har da hidimar wasanni na kasa da kasa, da hidimar yayata nasarorin wasannin Olympics, da hidimar shirya gasar wasanni da makamantansu. Kawo yanzu kuma, akwai kamfanoni 121 da suka tabbatar da halartar bikin, wanda hakan ya nuna an cimma burin daukar masu baje kolin dari bisa dari.” (Lubabatu Lei)