logo

HAUSA

Wang Yi ya yi tir da matakin Nancy Pelosi na ziyartar yankin Taiwan

2022-08-03 10:17:16 CMG Hausa

 

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya yi Allah wadai da ziyarar da kakakin majalissar wakilan Amurka Nancy Pelosi ta kai yankin Taiwan. Yana mai cewa, hakan keta manufar “kasar Sin daya tak a duniya” ne, kuma mataki ne da ya keta alfarmar ’yancin cin gashin kai na Sin, ya kuma haifar da rashin jituwa a siyasance, tare da fusata al’ummar kasar Sin, da Allah wadai daga sassan kasa da kasa.

Wang ya kara da cewa, abun da Pelosi ta yi ya nuna yadda wasu ’yan siyasar Amurka suka rungumi akidar gurgunta alakar Sin da Amurka, yayin da Amurkar ke kara zama babbar mai lahanta zaman lafiya a zirin Taiwan, tare da gurgunta yanayi na daidaito a shiyyar.

A daya hannun kuma, Wang ya gargadi Amurka, da ta kawar da mafarkin ta na dakile dunkulewar yankunan kasar Sin, kasancewar Taiwan bangare na kasar, kuma yanzu lokaci ne na dunkulewar Sin da ba wanda zai iya dakatarwa.

Ministan wajen na Sin ya ce, za a tabbatar da toshe duk wata kafa ta yunkurin samun ’yancin yankin Taiwan, da yunkurin duk wasu sassa na waje dake taimakawa hakan.

Ya ce duk irin yadda Amurka ta taimaka, ko ta yi hadin kai da masu burin ganin ’yancin kan Taiwan, ba za su yi nasara ba. Maimakon hakan, Amurka za ta bar tarihi ne na mummunan aikin tsoma hannu cikin harkokin gidan sauran kasashe. Batun Taiwan ya bijiro ne yayin da kasar ke da rauni, take kuma fama da tashe-tashen hankula, amma a yanzu farfadowar kasar Sin zai kawar da dukkanin wadannan kalubale.

A nasa bangare, mataimakin ministan harkokin wajen Sin Xie Feng ya kira jakadan Amurka a Sin Nicholas Burns a daren jiya Talata, inda ya gabatar da korafi mai karfi, da rashin amincewar Sin da ziyarar Nancy Pelosi a yankin Taiwan na kasar Sin. 

Sannan jakadan Sin a Amurka Qin Gang ya gabatar da korafi mai karfi, da rashin amincewar kasarsa ga majalissar tsaron mulkin Amurka ta White House, da ma’aikatar harkokin wajen kasar, game da ziyarar da kakakin majalissar wakilan kasar Nancy Pelosi ta kai yankin Taiwan na Sin.  (Saminu Alhassan)