logo

HAUSA

Ofishin MDD ya fitar da karin bayani game da batun harin jami’an wanzar da zaman lafiya a jamhuriyar dimokaradiyyar Congo

2022-08-03 13:37:58 CMG Hausa

 

A jiya Talata, ofishin MDD ya fitar da karin bayani, game da batun harbe-harbe da ake zargin wasu jami’an wanzar da zaman lafiya sun yi a jamhuriyar dimokaradiyyar Congo.

Da yake tsokaci kan al’amarin, kakakin sakataren MDD Stephane Dujarric ya ce, a ranar Lahadin karshen makon jiya, wasu dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD dake aiki a jamhuriyar dimokaradiyyar Congo sun yi yunkurin shiga iyakar kasar ta Congo bayan kammala hutun aiki, kuma hana su wannan dama ya tunzura su, har suka bude wuta da bindigogi, nan take kuma suka hallaka fararen hula 2, tare da jikkata wasu da dama.

Dujarric ya ce dakarun sojojin na aiki ne a karkashin rundunar MONUSCO, kuma bayan aukuwar wannan lamari, an tsare sojojin da suka aikata harbin. Duk da cewa Dujarric bai fayyace lambobi, da kasashen sojojin ba. Ya ce tuni aka tuntubi kasashen da suka fito, domin gaggauta gudanar da bincike na shari’a, kuma tuni MONUSCO ta ba da izinin ci gaba da binciken.

Yanzu haka dai akwai dakarun wanzar da zaman lafiya sama da 12,000 daga sama da kasashe 10, dake aiki a jamhuriyar dimokaradiyyar Congo.  (Saminu Alhassan)