logo

HAUSA

Sakatare janar na SCO ya yi tsokaci kan ziyarar Pelosy a Taiwan

2022-08-03 19:03:18 CMG Hausa

Zhang Ming, sakatare janar na kungiyar hadin kai ta shanghai wato SCO, ya ce manufar kasar Sin daya tak a duniya, matsaya ce da daukacin kasa da kasa suka amince da ita, haka kuma ita ce tushen huldar kasar Sin da kasashen waje.

Zhang Ming, ya bayyana haka ne a yau, lokacin da manema labarai suka yi masa tambaya game da ziyarar da kakakin majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosi ta kai Taiwan, inda ya kara da cewa, kungiyar hadin kai ta Shanghai, na nacewa ne ga manufar, kuma tana adawa da wasu kasashen su tsoma baki cikin harkokin gidan kasashe mambobinta. (Fa’iza Mustapha)