logo

HAUSA

Kalubalen da duniya ke fuskanta bai hana tattalin arzikin kasar Sin bunkasa a watanni shida na farkon bana ba

2022-08-03 11:00:05 CMG Hausa

Duk da tasirin annobar COVID-19 dake shafar tattali arziki da zamantakewa a duniya, da yanayi na rashin tabbas da ake fuskanta, tattali arzikin kasar Sin yana ci gaba da nuna juriya da bunkasa kamar yadda ake fata. Wannan nema ya sa mahukuntan kasar suka gabatar da jerin manufofin tabbatar da bunkasuwar tattalin arzikin kasar, wadanda suka taimaka wajen kara yin imani da kasuwar kasar, da kyautata yanayin cinikayya, har ma kamfanoni masu jarin waje suke kara nuna gamsuwa ga manufofin.

A baya-bayan nan ma, an gabatar da rahoton binciken yanayin cinikayyar kamfanoni masu jarin waje a kasar Sin a rubu’i na biyu na shekarar 2022, inda aka shaida cewa, kamfanoni masu jarin waje sun nuna kyakkyawar fata ga bunkasuwar kasar Sin da ma kasuwar kasar, da kuma nuna gamsuwa ga yanayin cinikayya da manufofin raya tattalin arzikin Sin. 

Bayanai na nuna cewa, kusan kashi 90 cikin kashi 100 na kamfanoni masu jarin waje sun nuna gamsuwa da manufofin samun wurin yin kasuwanci, da biyan haraji, da samun izinin shiga kasuwa, da manufofin kudi da rage haraji, da taimakawa kamfanonin wajen tinkarar yanayi mai sarkakiya yayin da ake yaki da cutar COVID-19, da kuma saukin aiwatar da manyan ayyuka masu amfani da jarin waje a kasar Sin.

Alkaluma na nuna cewa, ribar manyan masana’antun kasar Sin ta karu da kaso daya bisa dari a watanni 6 na farkon bana, babban jami’i a hukumar kididdigar kasar NBS Zhu Hong ya alakanta wannan ci gaba, da matakan aiwatar da cikakkun tsare-tsaren shawo kan annobar COVID-19, da na raya tattalin arziki da ci gaban al’umma, da kuma matakai daban daban da aka aiwatar, domin saita akalar tattalin arzikin kasar. 

Bugu da kari, yawan GDPn kasar a farkon watanni 6 na bana, ya kai kudin Sin Yuan biliyan 56264.2, wanda ya karu da kashi 2.5% bisa na makamancin lokaci na bara. Daga cikinsu, sha’anin gona da na masana’antu da ba da hidimma, sun samu karuwar da yawansa ya kai Yuan biliyan 2913.7 da Yuan biliyan 22863.6 da Yuan biliyan 30486.8. Wanda ya karu da kashi 5.0% da kashi 3.2% da 1.8% bisa na makamancin lokaci na bara.

Hakazalika, manyan kamfanoni mallakar gwamnatin tsakiya ta kasar Sin, sun ba da babbar gudummawa wajen zuba jari, inda sauran kamfanonin sana’o’i daban daban na kasar suka ci gajiya. Wannan na nuna cewa, sun taimaka matuka ga bunkasar tattalin arzikin kasar Sin cikin watanni shida na farkon bana. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)