logo

HAUSA

Sassa da dama sun yi Allah wadai da ziyarar Pelosi a yankin Taiwan

2022-08-03 15:29:17 CMG Hausa

Duk da rashin amincewa da kasar Sin ta nuna da babbar murya, kakakin majalisar wakilan kasar Amurka Nancy Pelosi ta kare aniyarta ta zuwa yankin Taiwan na kasar Sin a jiya Talata da dare, kuma dangane da hakan, gwamnatocin kasashe da dama da suka hada da Rasha da Iran da Syria da Palasdinu da Nicaragua da sauransu sun fitar da sanarwoyi, inda da kakkausan harshe ne suka yi Allah wadai da matakin, tare da jaddada matsayarsu ta bin manufar kasar Sin daya tak a duniya.

Baya ga haka, gwamnatin yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin ma ta bayyana rashin amincewarta da matakin da Pelosi ta dauka tare da la’antarta da babbar murya.

A yau 3 ga wata kuma, rundunar ’yantar da jama’ar kasar Sin reshen gabashin kasar ta kaddamar da atisayen soja a yankunan teku da ma sararin sama na kewayen tsibirin Taiwan. (Lubabatu)