logo

HAUSA

Sin ta karbi shugabancin karba karba na kwamitin sulhun MDD

2022-08-02 14:43:24 CMG Hausa

Kasar Sin ta karbi shugabancin karba karba na kwamitin sulhun MDD na watan Agusta a jiya Litinin, kuma zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Zhang Jun ya jagoranci shawarwari a tsakanin kwamitin sulhun, inda aka zartas da ajandar aiki na kwamitin na wannan wata.

Bisa ajandar, kwamitin sulhu zai tattauna batutuwan da suka shafi kasashen Yemen da Syria da yaki da ta’addanci da sauransu. Bisa shawarar da kasar Sin ta gabatar, kwamitin zai kuma shirya wasu tarukan musamman biyu dangane da “kiyaye tsaron bai daya” da “inganta karfin kasashen Afirka”.

A wannan rana, Mr. Zhang Jun ya kuma kira taron manema labarai, inda ya ce, kasar Sin na kokarin ingiza ajandar bunkasuwa ta MDD, inda ta cimma burin kawar da talauci shekaru 10 kafin shekarar 2030, baya ga shawarar bunkasa kasashen duniya da shugaban kasar ya gabatar, matakin da ya ba da gudummawa ga cimma burin tabbatar da dauwamammen ci gaba nan da shekarar 2030, da daidaita matsalar abinci a duniya da kuma matsalar rashin daidaiton bunkasuwar sassa daban daban. Ban da haka, kasar Sin za ta yi kokarin cimma kololuwar fitar da yawan hayaki mai dumama yanayi kafin shekarar 2030, tare da samun daidaito tsakanin yawan hayakin da za ta fitar da yawan abubuwan da za su shawo kan sa kafin shekarar 2060. Wannan aiki yana da matukar wahala, da bukatar sadaukarwa mai yawa, amma Sin za ta yi abin da ta ce wajen ganin ta cika alkawarinta.