logo

HAUSA

Wang Yi zai halarci taron hadin gwiwar ministocin wajen Sin da kasashen gabashin Asiya a Cambodia

2022-08-02 19:23:44 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta ce babban dan majalissar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, zai halarci taron hadin gwiwar ministocin wajen kasar Sin da kasashe mambobin kungiyar ASEAN, da na mambobin ASEAN da ministocin karin wasu kasashe 3, da na Sin da na gabashin Asiya, da taron ministocin wajen kasashen gabashin Asiya, da taron dandalin ASEAN, tarukan da za su gudana a birnin Phnom Penh na kasar Cambodia, tsakanin ranekun 3 zuwa 5 ga watan nan na Agusta.

Kaza lika Hua ta ce Mr. Wang zai gudanar da rangadi a Cambodia, bisa gayyatar da mataimakin firaministan kasar, kuma ministan wajen kasar Prak Sokhonn ya yi masa. (Saminu Alhassan)