logo

HAUSA

Wakilin Sin a MDD ya kira ziyarar da Pelosi za ta kai yankin Taiwan a matsayin tsokana

2022-08-02 15:56:47 CMG Hausa

Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya yi karin haske kan matsayin kasar Sin game da batun yankin Taiwan da kuma yiyuwar ziyarar da kakakin majalisar dokokin Amurka Nancy Pelosi za ta kai yankin, yana mai cewa irin wannan ziyarar "da alama tana da hadari kuma tsokana ne."

Zhang ya shaida wa manema labarai cewa, "Manufar Sin daya tak a duniya, wani jan layi ne a huldar da ke tsakanin Sin da sauran kasashe, kuma ba za mu bar wani ya ketare wannan jan layi ba." (Ibrahim Yaya)