logo

HAUSA

Sin: SCO na da makoma mai haske

2022-08-01 20:38:44 CMG HAUSA

 

A yau Litinin ne mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya amsa tambayoyin da aka yi masa, a gun taron manema labarai, inda ya tabo batun taron ministocin harkokin waje na kungiyar hadin kai ta Shanghai ko SCO a takaice, wanda ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya halarta a birnin Toshkent, hedkwatar Uzbekistan a ran 29 ga watan da ya shude.

Zhao ya yi tsokaci game da shawarwari guda 5 da Wang Yi ya gabatar a yayin taron, da suka hada da bukatar hadin kan kasashe mambobin SCO, da inganta tsaron shiyyar su, da kuma ingiza samun ci gaba mai dorewa, da nacewa, da gudanar da harkoki tsakanin bangarori daban-daban, da kuma sa kaimi ga gina tsare-tsaren kungiyar.

A cewarsa, Sin ta amince da makomar SCO, kuma akwai alamun za a samu bunkasuwa mai kyau a nan gaba. (Amina Xu)