logo

HAUSA

Jirgin C919 na kasar Sin ya kammala gwajin ingancin tashi

2022-08-01 14:39:07 CMG Hausa

 

Kamfanin kera jiragen sama na kasar Sin (COMAC) Litinin din nan, ya sanar da cewa, babban jirgin saman fasinja na farko da kasar Sin ita kanta ta kera, da zai shiga kasuwa, samfurin C919, ya kammala gwajin tashi cikin nasara, don tabbatar da ingancinsa a sararin samaniya, matakin da ya share hanyar kara samar da shi da ma shiga kasuwa.

A watan Maris din shekarar 2021 ne, kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na China Eastern Airlines, daya daga cikin manyan kamfanonin jiragen sama na kasar Sin mai halkwata a birnin Shanghai, ya rattaba hannu kan wata kwangilar sayen jiragen na C919 guda biyar, yarjejeniyar kasuwanci ta farko game da jirgin.

Daga cikin kasuwannin zirga-zirgar jiragen sama mafi saurin bunkasuwa a duniya, kasar Sin ta kera nata jirgin samfurin C919, don yin gogayya da manyan jiragen saman fasinja masu matsakaicin zango, irin su A320 kirar Airbus da Boeing 737 MAX.

Jirgin na C919 yana da kujeru 158 zuwa 174, madaidaicin tafiyar kilomita 4,075 da kuma iyakar kilomita 5,555. (Ibrahim)