logo

HAUSA

Rundunar sojin saman kasar Sin ta lashi takobin kare cikakken ‘yanci da yankunan kasar

2022-07-31 16:26:31 CMG Hausa

Rundunar sojin saman kasar Sin, ta ce hakki ne kan kowanne sojan samar kasar, ya kare yankuna da ikon kasarsa.

Kakakin rundunar Shen Jinke ne ya bayyana haka, yayin wani taron manema labarai da aka yi yau Lahadi.

A cewarsa, kudurin rundunar ne kare cikakken ‘yanci da yankunan kasar Sin, bisa jajircewa da dogaro da kai. (Fa’iza Mustapha)