logo

HAUSA

An bude rumbun adana wallafe -wallafe da al’adun gargajiya na kasar Sin

2022-07-31 16:20:36 CMG Hausa

An kaddamar da ginin rumbun adana wallafe-wallafe da al’adun gargajiya na kasar Sin a jiya a Asabar. Ginin wata muhimmiyar alama ce ta al’adun gargajiya a sabon zamani, haka kuma cibiyar adana al’adun gargajiya ta kasar Sin. Bayan budewar, zai gudanar da ayyukan wallafa da adana muhimman kayayyaki da al’adun gargajiya da aka yi gado. Babban daki mai lamba 1 na ginin, ya kaddamar da jerin nune-nune na musammam bisa taken raya tarihin Sinawa da ci gaban wayewarsu. Haka kuma yana haska sauye-sauyen tarihi da shaida nasarorin da aka cimma. (Fa’iza Mustapha)