logo

HAUSA

An yi wa wani bakar fata duka har lahira a tsakiyar birnin kasar Italiya

2022-07-31 20:38:04 CMG Hausa

An yi wa wani dan Nijeriya mai sayar da abubuwa a bakin titi duka har lahira a tsakiyar birnin kasar Italiya, yayin da ‘yan kallo suka gaza shiga tsakani.

‘Yan sanda sun cafke wani dan kasar Italiya bayan hoton bidiyon lamarin ya yi ta yawo a shafukan yanar gizo na kasar da kafafen sada zamunta, lamarin da ya haifar da ya harzuka mutane. (Fa’iza Mustapha)