logo

HAUSA

Za a wallafa jawabin Xi game da kafuwar PLA a mujallar Qiushi

2022-07-31 16:09:53 CMG Hausa

Za a wallafa wani muhimmin jawabi mai taken “Murnar cika shekaru 90 da kafuwar rundunar PLA wato rundunar sojojin ‘yantar da al’ummar kasar Sin” da Xi Jinping, babban sakataren kwamitin kolin JKS, kuma shugaban kasa, kana shugaban hukumar aikin sojin kasar Sin ya gabatar, a cikin mujallar “Qiushi” a gobe Litinin, 1 ga watan Agusta.

Cikin jawabinsa, shugaba Xi ya jaddada cewa, ba za a manta da tarihin rundunar sojojin kasar Sin ba har abada, inda ya ce raya tarihin zai kara karfafa gwiwar Sinawa, ta yadda za su farfado da al’ummun Sinawa yadda ya kamata, tare kuma da hanzarta gina rundunar sojojin kasar da ta kai sahun gaba a fadin duniya.

Xi ya kara da cewa, a ko da yaushe, kasar Sin tana ba da gudumowa  wajen wanzar da zaman lafiya a fadin duniya, da ciyar da duniya gaba, da kuma kiyaye tsarin kasa da kasa, kana har kullum, rundunar sojojin kasar Sin tana taka muhimmiyar rawa kan shimfida zaman lafiya a duniya. Ya ce a nan gaba, rundunar sojojin kasar Sin za ta ci gaba da gudanar da hadin gwiwa da cudanya tsakaninta da sauran kasashen duniya, domin dakile kalubalen tsaron dake adabar duniya, tare kuma da ingiza ginin kyakkyawar makomar bil adama ta bai daya yadda ya kamata. (Jamila)