logo

HAUSA

Kasuwanci bangaren da ba na masana’antun kira ba a Sin ya ci gaba da farfadowa a watan a Yuli

2022-07-31 15:55:48 CMG Hausa

Hadaddiyar kungiyar jigilar kayayyaki da ta masu sayayya ta kasar Sin da cibiyar binciken ayyukan hidima ta hukumar kididdiga ta kasar, sun sanar a yau Lahadi da cewa, alkaluman harkokin kasuwanci da ba na masana’antun kira ba, sun kai kaso 53.8 bisa dari a watan Yuli, adadin ya karu da kaso 0.5 bisa dari idan aka kwatanta shi da na makamancin lokacin a bara, wato ya kai sama da matsakaicin matsayin rabin farkon bana.

Alkaluma game da ma’aikatan harkokin kasuwancin ba ta sauya sosai ba, kuma ayyukan hidima na ci gaba da farfadowa. A takaice dai, ana iya cewa, harkokin kasuwanci da ba na mana’antun kira ba a kasar Sin, suna kara farfadowa sakamakon manufofin gwamnatin kasar da raguwar tasirin annobar COVID-19.

Ban da haka, ana samar da guraben ayyukan yi a fadin kasar yadda ya kamata, kana matsin lambar da kamfanoni ke fuskanta yana kara saukaka. Haka kuma, ana samun karuwar zuba jari, sannan ana sayar da hajoji lami lafiya, bugu da kari, aikin hidima dake bukatar cudanyar mutane yana farfadowa cikin sauri. (Jamila)