logo

HAUSA

Ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ta yi bayani game da dokar da ta tanadi damar samar da rukunin ababen hada na’urorin laturoni ta Amurka

2022-07-30 16:13:26 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ya bayyana a jiya cewa, a kwanakin baya, majalisar dattawan Amurka, ta zartas da shirin dokar da ta tanadi damar samar da rukunin ababen hada na’urorin laturoni, wadda ta samar da tallafin kudi ga kamfanonin Amurka dake kera na’urorin laturoni, babu shakka wannan manufa ce ta nuna goyon baya ga sha’anin kasar Amurka da kanta. Kana shirin dokar ta kayyade wasu kamfanoni yin ciniki da zuba jari a kasar Sin, hakan zai kawo illa ga sana’ar a duniya da ma ciniki a duniya. Don haka, kasar Sin ta mai da hankali sosai kan wannan batu.

Kakakin ya bayyana cewa, ya kamata a aiwatar da dokar da Amurka ta zartas bisa ka’idojin kungiyar cinikayya ta duniya wato WTO da kuma ka’idojin bude kofa, da nuna gaskiya da rashin nuna bambanci, kuma hakan zai taimaka wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiyar tsarin masana'antu da na samar da kayayyaki a duniya da kuma kaucewa rarrabuwar kawuna. Kasar Sin za ta ci gaba da mai da hankali kan ci gaba da aiwatar da shirin dokar, da daukar kwararan matakai don kiyaye moriyarta idan bukatar hakan ta taso. (Zainab)