logo

HAUSA

An tattauna tsakanin shugaba Xi na Sin da Biden na Amurka

2022-07-29 11:13:49 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tattauna ta wayar tarho da takwaransa na Amurka Joe Biden, inda suka tabo batutuwan da suka shafi dangantakarsu, da ma sauran batutuwan da suke da moriya iri guda.

Tattaunawar ta gudana ne jiya Alhamis bisa rokon shugaban Amurka, Joe Biden.

Yayin tattaunawar, shugaba Xi Jinping ya ce duniya a yanzu na fuskantar matsaloli da sauye-sauye da gibi wajen samun ci gaba da rashin tsaro dake karuwa. Ya kara da cewa, yayin da ake fuskantar sauye-sauye da tashin hankali, kasa da kasa da al’ummominsu a fadin duniya, na sa ran Sin da Amurka za su ja gaba wajen daukaka zaman lafiya da tsaro da inganta samar da ci gaba da kwanciyar hankali a duniya.

Har ila yau, ya ce bangarorin biyu na bukatar hada hannu wajen rage rikice-rikice a yankunan da taimakawa wajen kawo karshen annobar COVID-19 nan ba da jimawa ba, da rage hadarin hauhawar farashin kayayyaki da rashin aikin yi da tabarbarewar tattalin arziki da kare tsari da dokokin kasa da kasa karkashin jagorancin MDD.

Bugu da kari, shugaba Xi ya ce matsayin kasarsa kan batun Taiwan bai sauya ba, kana tabbatar da kare cikakken ’yanci da yankunan kasar Sin, muradi ne mai karfi na al’ummar Sinawa sama da biliyan 1.4.

A nasa bangaren, shugaba Joe Biden ya ce duniya na kan wata muhimmiyar gaba, kuma hadin gwiwar Sin da Amurka ba al’ummomin kasashen biyu kadai zai amfanawa ba, har ma da jama’ar dukkan kasashen duniya.

Ya ce Amurka na fatan barin kofar tuntubar juna tsakaninta da Sin a bude, domin inganta fahimtar juna da kaucewa rashin fahimta da hada hannu a bangarorin da suke da moriya ta bai daya da kuma tafiyar da bambancin dake tsakaninsu yadda ya kamata.

Ya kuma nanata cewa, manufar kasar Sin daya tak a duniya ba ta sauya ba a wajen Amurka, kuma ba za ta sauya ba, kana Amurka ba ta goyi bayan ’yancin kan yankin Taiwan. (Fa’iza Mustapha)