logo

HAUSA

Kasar Sin ta bukaci a girmama cikakken ’yancin kasashen da suka taba fama da rikici

2022-07-28 10:38:37 CMG Hausa

Zaunannen wakilin Sin a MDD Zhnag Jun, ya yi kira ga kasa da kasa su girmama cikakken ’yancin kasashen da suka taba fama da rikici.

Zhang Jun ya fadawa taron kwamitin Sulhu kan hukumar wanzar da zaman lafiya cewa, akwai bukatar kasa da kasa su girmama cikakken ’yanci da ikon kasashen da suka yi fama da rikici, tare da taimaka musu bisa amincewa da kuma bukatarsu.

Ya kuma yi kira ga MDD da kasa da kasa, su taimakawa kasashen da batun ya shafa, musammam gwamnatocinsu, wajen karfafa tsarin shugabanci da samun ci gaba mai dorewa da tabbatar da tsaro da juriya.

Da aka tabo batun kudin taimakawa samar da zaman lafiya, jakadan na kasar Sin ya ce kasarsa na goyon bayan samar da tallafin kudin da ake bukata wajen samar da zaman lafiya ta mabambantan hanyoyi.

Bugu da kari, ya ce kasar Sin ta bada taimako da dama ga asusun wanzar da zaman lafiya na MDD (PBF), tare da tallafin kudi ga shirye-shiryen wanzar da zaman lafiya, karkashin shirin samar da ci gaban duniya da asusun kungiyar kasashe masu tasowa da asusun wanzar da zaman lafiya da ci gaba na MDD da Sin. Yana mai cewa, kasarsa za ta ci gaba da taimakawa ta hanyar ingantattun matakai tare da bada gudunmawa da zummar samun zaman lafiya mai dorewa. (Fa’iza Mustapha)