logo

HAUSA

Iran na maraba da karin matakan diflomasiyya domin farfado da yarjejeniyar nukiliyarta

2022-07-28 14:11:30 CMG Hausa

Ministan harkokin wajen Iran Hossein Amir-Abdollahian, ya ce kasarsa na maraba da ci gaba da daukar matakan diflomasiyya da tattaunawa, domin ceto yarjejeniyar nukiliyarta.

Shafin yanar gizo na ma’aikatar harkokin wajen kasar, ya ruwaito cewa, Amir Abdullahian ya bayyana haka ne yayin da zantawarsa ta wayar tarho da Joseph Borrell, babban mai tsara manufofi na Tarayyar Turai, bayan jami’in ya gabatar da wani sabon daftari na farfado da yarjejeniyar.

A cewar ministan na Iran, kasarsa ta kuduri niyyar cimma ingantacciyar yarjejeniya mai dorewa, yana mai bukatar Amurka ta nemi hanya mafi dacewa ta kawo mafita da cimma yarjejeniya.

Ya ce Amurka ta kan yi ikirarin son cimma yarjejeniya, a don haka ya bukaci furucin ya kasance cikin kunshin yarjejeniyar sannan kuma a aikace. (Fa’iza Mustapha)