logo

HAUSA

An gudanar da taron tattaunawa na wakilan jam’iyyu daban daban

2022-07-28 21:19:24 CMG Hausa

Kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta Sin, ya gudanar da taron karawa juna sani, kan yanayin tattalin arziki a halin yanzu da shirin raya tattalin arziki na watanni 6 na karshen shekarar bana, inda aka saurari ra’ayoyi da shawarwari daga wakilan jam’iyyu daban daban na kasar Sin da shugaban kungiyar hadin gwiwar masana’antu da cinikayya da kuma mutanen da ba sa cikin jam’iyya. Babban sakataren kwamitin tsakiya na JKS Xi Jinping ne ya shugabanci taron, inda ya yi jawabin cewa, akwai sharuda masu kyau wajen bunkasa kasar Sin, kana ana iya tinkarar matsalolin tattalin arziki da samun kyakkyawar makoma a wannan fanni.

Xi Jinping ya bayyana cewa, tun daga farkon shekarar bana, Sin ta gudanar da ayyukan yaki da cutar COVID-19 cikin nasara, da bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al’umma, kuma an samu sabon ci gaba a fannonin tattalin arziki da zamantakewar al’umma, kasar Sin baki daya ta yi namijin kokarin samun kyakkyawan sakamako.

Xi Jinping ya jaddada cewa, ya kamata a ci gaba da rigakafin annobar COVID-19, da daidaita tattalin arziki, da samun ci gaba bisa tsari na bai daya, da karfafa farfadowar tattalin arziki, da kokarin cimma kyakkyawan sakamako. (Zainab)