logo

HAUSA

Kasashe mambobin RCEP suna sa ran cin gajiya daga kasuwar sayayyar kasar Sin

2022-07-28 14:17:13 CMG Hausa

Yanzu haka ana ci gaba da gudanar da bikin baje kolin hajojin kasa da kasa a birnin Haikou na lardin Hainan dake kudancin kasar Sin, don haka kamfanonin kasashen da suka daddale yarjejeniyar kafa huldar abokantakar tattalin arzikin shiyya shiyya daga duk fannoni wato RCEP a takaice, suke kara mai da hankali kan dandalin baje kolin, ta yadda za su kara zurfafa hadin gwiwa tsakaninsu da kasar Sin.

An lura cewa, a karon farko, kasashen Sin da Japan, sun kafa huldar cinikayya maras shinge dake tsakaninsu bisa yarjejeniyar ta RCEP, kuma rumfunan baje kolin hajojin da aka kebewa kamfanonin Japan sun fi na sauran kasashe mambobin RCEP girma, wato sun karu daga muraba’in mita 2000 a bara, zuwa muraba’in 3500 a bana.

Babban wakilin hukumar Jetro ta kasar Japan Kenji Shimizu ya bayyana cewa, kamfanoni matsakaita, da kanana na kasarsa, suna fatan za su samu iznin shiga kasuwar kasar Sin ta hanyar halartar bikin baje kolin hajojin, yana mai cewa, “Hajojin da kamfanoninmu suka baje kolin su a bikin suna da yawan gaske, mun san kasuwar sayayya ta kasar Sin za ta kara habaka, don haka muke fatan kamfanoninmu za su iya samun damar shiga kasuwar kasar Sin ta hanyar halartar wannan bikin baje koli.” (Jamila)