logo

HAUSA

Kwararre a wasan saukar lema ya shaida ci gaban da wasan ke samu a kasar Sin

2022-07-28 16:00:15 CRI

Yayin da samaniya ta yi shudi a lokacin zafi, a sararin samaniyar lardin Hainan, wani jirgin helkwafta na kewaye a tsayin da ya kai mita 4,000. Wannan jirgi na dauke da kwararre a wasan saukar lema mai suna Nam Lee, wanda ke taimakawa masu yawon bude ido dake zuwa lardin domin gwada wannan wasa mai kayatarwa.

Nam mai shekaru 36 da haihuwa dan asalin Koriya ta kudu ne, yana kuma da kwarewa matuka, inda kawo yanzu ya yi saukar lema sama da sau 9,000 tun fara sana’ar ta sa. Ya kuma koma birnin Sanya, na lardin tsibirin Hainan ne a watan Satumbar shekarar 2021, inda a yanzu haka yake aiki da kamfanin wasan saukar lema mai suna “Tarhe”.

Wannan wasa mai cike da kasada dai a iya cewa sabo ne a kasar Sin, amma sannu a hankali yana samun karin karbuwa, inda gudummawar mutane irin su Nam ke samun matukar yabo. Baya ga karawa masu sha’awar wasan karsashi da Nam ke haifarwa, a hannu guda kuma, yana da kwarewa a matakai masu yawa, dake taimaka masa wajen raya wasan a kasar Sin cikin yanayi na tsaron lafiyar masu yin wasan a kasar Sin.

Da fari dai Nam ya samu shaidar shiga wasan ne a shekarar 2009, lokacin da yake dalibta a kwaleji, inda ya samu lasisin wasan daga hukumar kula da wasan saukar lema ta Amurka. Daga bisani a shekarar 2020, bayan ya cimma nasarar yin dubban saukar lema ba tare da matsala ba, ya samu shaidar kwarewa ta hukumar lura da harkokin sufurin samaniya ta Amurka. Wannan shaida ce dake tabbatar da cewa, mai dauke da ita zai iya tsara kayayyakin da ake amfani da su wajen saukar lema, kamar nau’oin damara da ake amfani da su yayin sauka daga samaniya.

A yanzu, Nam ya zama jigo a fannin tabbatar da ingancin kayan da ake amfani da su wajen saukar lema, inda yake taimakawa sauran masu lura da aikin wajen jagorantar masu yawon bude ido, wadanda ke zuwa yin wasan a samaniyar birnin Sanya. Wani muhimmin fanni da yake lura da shi a kamfanin da yake aiki, shi ne tabbatar da tsaron lafiyar masu saukar lema. Nam na da tabbacin cewa, wasan yana da tsaro muddin an yi komai bisa ka’ida.

A duk ranar aiki, Nam yana duba lemomin da ake amfani da su a wurin ajiyar su. Bayan ya duba da kyau, sai ya yi musu alama da lau’in ja, domin sauran ma’aikata su gane su.

Yana kuma kula sosai da lemomin da ake ajiyewa domin bukatar gaggawa ta maye gurbi, idan lemar da ake amfani da ita ta samu matsala. Ba tare da la’akari da ko an yi amfani da lema ba ko a’a, Nam yana sake duba ko wacce lema bayan duk kwanaki 180. Yana shafe kusan sa’oi 6 kafin gama duba duk lema guda daya ta amfanin gaggawa.

Dukkanin lemomin da ake amfani da su a wurin aikin Nam, ana duba su da kyau akai-akai, domin tabbatar da za su iya jure wahalar aikin. Ana yi musu gwaji na musamman, ko da kuwa ba a yi amfani da su a tsawon lokaci ba. Idan aka gano lema na da wata illa, ta yadda ba za ta iya jure karfin da ya kai kilogiram 14 zuwa 18 cikin sama da dakika 3 ba, sai a daina amfani da ita nan take.

Babban manajan kamfanin saukar lema na “Tarhe” Zhang Enming, ya ce gwajin tabbatar da nagartar lemomin da suke amfani da su, yana kara tsadar kudin da kamfanin ke kashewa, amma kuma yana tabbatar da tsaron lafiyar masu zuwa yin wasan, da kuma ma’aikatan dake taimaka musu. Duk da cewa ko wace lema daya tana kaiwa sama da kudin Sin yuan 30,000, kimanin dalar Amurka 4,400.

Zhang ya kara da cewa, "Nam ya zama kashin bayan ayyukan kamfanin mu" da tallafin sa yanzu ba na shakkar ingancin lemomin da muke amfani da su".

A shekarun baya bayan nan, sana’ar saukar lema na ta samun karin karbuwa, inda alkaluman kididdigar hukumar dake lura da wasannin samaniya suka nuna cewa, a shekarar 2021 kadai, an yi saukar lema da ta kai 12,000 a lardin na Hainan.

Babbar sakatariyar hukumar Xu Liwen, ta ce a yanzu, Nam ya zama daya daga kwararru ‘yan kasashen waje, dake aiki a hukumar lura da wasannin saukar lema ta kasar Sin. Xu ta yi imanin cewa, nan gaba karin kwararru za su yi sha’awar zuwa tsibirin domin shiga wannan wasa, musamman saboda kyakkyawan yanayin da aka samu, na kafuwar yankin ciniki maras shinge na tashar ruwan Hainan.

Nam bai yi dana-sanin komowa kasar Sin ba, yana kuma yin cikakken amfani da lokacin sa a kasar, wajen koyon Sinanci, da kulla abota, da kuma cudanya da al’adun kasar Sin. A nan gaba kuma, yana fatan ci gaba da samun nisashi a Sanya, tare da cin gajiya sosai daga kwarewarsa ta wasan saukar lema. (Saminu Alhassan)