logo

HAUSA

Ribar masana’antun Sin ta karu da kaso 1 bisa dari a rabin farko na bana

2022-07-27 13:34:29 CMG Hausa

Ribar manyan masana’antun kasar Sin ta karu da kaso daya bisa dari a rabin farko na shekarar bana, kamar yadda alkaluman kididdiga da aka fitar a yau Laraba suka tabbatar da hakan.

Babban jami’i a hukumar kididdigar kasar NBS Zhu Hong, ya alakanta wannan ci gaba, da matakan aiwatar da cikakkun tsarukan shawo kan annobar COVID-19, da na raya tattalin arziki da ci gaban al’umma, da kuma matakai daban daban da aka aiwatar, domin saita akalar tattalin arzikin kasar.  (Saminu Alhassan)