logo

HAUSA

Sin na fatan kiran taron kasa da kasa kan yunkurin shimfida zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya

2022-07-27 10:51:49 CMG Hausa

Jiya Talata, mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Geng Shuang ya bayyana cewa, kasar Sin na fatan kiran taron shawarwari domin shimfida zaman lafiya, inda za a gayyaci mambobin kwamitin sulhu na MDD, da dukkanin bangarorin da yunkurin shimfida zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya ya shafa, domin lalubo hanyar siyasa mafi dacewa don warware matsalar Falesdinu.

Yayin taron muhawara kan batun yankin Gabas ta Tsakiya da Falesdinu na kwamitin sulhun MDD, Geng Shuang ya ce, matsalar Falesdinu ta shafi zaman lafiya da zaman karko a fadin yankin Gabas ta Tsakiya, don haka ya kamata gamayyar kasa da kasa su gaggauta yin aikin warware matsalar Falesdinu yadda ya kamata.

Ya kuma kara da cewa, ya kamata gamayyar kasa da kasa su mai da hankali kan bukatun Falesdinu da Isra’ila cikin yanayin adalci, kuma ya kamata Isra’ila ta sauke nauyin dake wuyanta na kare tsaron al’umma a yankunan da ta mamaye.

Bugu da kari, ya ce kasar Sin tana goyon bayan kasashen dake yankin Gabas ta Tsakiya, ta fuskar warware matsalar tsaro cikin hadin gwiwa, kuma tana goyon bayan al’ummomin yankin, a kokarinsu na neman hanyar ci gaba cikin ’yanci.

Ya ce kasar Sin ta yi hadin gwiwa da kasashen dake yankin wajen yaki da annobar cutar COVID-19, da aiwatar da shawarar “Ziri daya da hanya daya” cikin hadin gwiwa, domin ba da gudummawa ga kasashen yankin wajen neman bunkasuwa. Kaza lika kasar Sin na fatan ba da karin gudummawa ga kasashe a fannin shimfida zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya baki daya. (Maryam Yang)